Connect with us

Labarai

Sojoji sun yi luguden wuta a jihohin Katsina da Sokoto

Published

on

Dakarun Operation Hadarin Daji na sojojin ƙasar nan sun yi luguden wuta kan sansanonin ‘yan bindiga a cikin dazukan Jihohin Sokoto da kuma Katsina, tare da hallaka 34 da kuma jikkata wasu 20.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa sojojin sun yi luguden wutar ne ta jiragen sama.

Yankunan da suka yi luguden wutar kuwa su ne Mashema da ‘Yanfako da Geɓe da kuma Gatawa, duk a kananan hukumomin Isa da kuma Sabon Birni da ke Jihar Sokoto.

Sai kuma wasu yankuna na karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!