Labarai
Ba za mu dena yajin aiki ba sai gwamnati ta biya mana bukatun mu – ASUU
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta sanar da cewa za ta ci gaba da yajin aikin da take yi har sai gwamnatin tarayya ta biya mata dukkan bukatunta.
Shugaban kungiyar Farfesa Biodun Ogumyemi ne ya bayyana hakan a jami’ar garin Fatakwal da ke jihar Rivers, lokacin taron masu ruwa da tsaki domin sanar da al’ummar kasar nan muradensu, yana mai cewar wajibi ne gwamnantin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar cimma da suka a cikin shekarar 2012.
Ya kara da cewa bukatunsu na ciyar da kasar nan gaba ne tare da kyautata harkokin koyo da koyarwa, wanda daliban jami’o’i a kasar nan za su ci moriyarsu matukar aka aiwatar.
A don haka ne ya bukaci daliban su kara hakuri da halin da ake ciki a yanzu na yajin aikin.
Farfesa Ogunyemi ya ce har yanzu malaman jami’o’in kasar nan na karbar albashi ne bisa tsarin da aka dora su a kai na shekarar 2009, wanda hakan ya nuna cewar babu wani gyara da aka yi a kan abinda suka nema.
You must be logged in to post a comment Login