Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Hukumar Hizbah a jihar Jigawa ta lalata kwalaben barasa

Published

on

Hukumar Hizbah ta Jihar Jigawa ta ce ta lalata kwalaben barasa guda 588 da kwace a karamar huumar Ringim ta Jihar.

Kwamandan hukumar Malam Ibrahim Dahiru ne ya shaida hakan yau yayin zantawa da manema labarai a birnin Dutse, yana mai karin hasken cewa sun gudanar da aikin ne a ranar alhamis din da ta gabata.

Malam Ibrahim Dahiru ya ce shan barasa a Jihar baki-daya haramun ne, a don hakan hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu aikata miyagun dabi’u a Jihar, ciki har da masu ta’ammali da barasa.

Sannan kuma ya shawarci al’ummar jihar da su kaucewa aikata munanan ayyukan da ka iya lalata rayuwarsu da ta sauran al’umma.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!