Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba za mu iya kakkabe ‘yan ta’adda daga kasar nan ba, idan ba mu da makamai – Janar Attahiru

Published

on

Babban hafsan sojin kasa na kasar nan laftanal janar Ibrahim Attahiru, ya ce, zai yi matukar wuya dakarun kasar nan su samu nasarar kakkabe ‘yan ta’adda daga kasar nan baki daya ba tare da samun makamai ba.

A cewar janar Attahiru rundunar sojin kasar nan tana bukatar makamai na zamni wadanda za ta yaki masu satar mutane suna garkuwa da su da ‘yan kungiyar boko haram.

Laftanal janar Ibrahim Attahiru ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ‘yan kwamitin kula da rundunar sojin kasar nan na majalisar dattawa karkashin jagoranci sanata Ali Ndume wadanda suka kai masa ziyara ofishinsa a jiya laraba.

Babban hafsan sojin ya kuma bukaci majalisun dokokin tarayya da su dauki batun makaman da muhimmanci domin hakan ne kawai zai kawo karshen ayyukan batagari a Najeriya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!