Addini
Ba za mu lamunci ci gaba da kisan ƴan arewa da IPOB ke yi ba – ƙungiyar Arewa
Wata ƙungiya da ke rajin kare martabar arewacin ƙasar nan mai suna Northern Reform Organzation ta yi tir da ci gaba da kisan kiyashi da ake yiwa al’ummar arewacin ƙasar nan mazauna kudu.
A cewar ƙungiyar ta NRO, ta’addanci da haramtacciyar ƙungiyar da ke rajin kafa ‘yan tacciyar ƙasar Biafra ta IPOB ke yi ga al’ummar arewa mazauna jihohin kudu maso gabashi, lamari ne da ‘yan arewa ba za su lamunta ba.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da ƙungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun sakatare janar na ƙungiyar Alhaji Abdulkadir Yusuf Gude.
Sanarwar ta kuma bukaci al’ummar arewa da su ci gaba da zama da juna lafiya duk kuwa da banbancin addini da ke tsakaninsu.
Haka kuma sanarwa ta buƙaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su yi duk me yiwuw don kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Yayin da a bangare guda ƙungiyar ta taya al’ummar musulmin ƙasar nan dama na duniya baki ɗaya murnar kammala azumin watan ramadan da kuma bikin ƙaramar sallah.
You must be logged in to post a comment Login