Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ba za mu sanya dokar kulle a wannan lokaci ba -Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce bata da shirin sanya dokar kulle duk da karuwar annobar corona da ake samu a kwanakin nan.

Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire yayin taron ministoci na mako -mako da ake gudanarwa a Abuja.

Dakta Osagie Ehanire, ya ce adadin masu kamuwa da cutar bai kai ace an sanya dokar kulle ba.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da NCDC ta ce alkaluman wadanda suka kamu da cutar a ranar laraba sun kai mutum 790, adadin shi ne mafi yawa da aka samu cikin watanni shida.

NCDC ta ce cutar corona samfurin Delta ta fi saurin yaduwa da kuma saurin yin kisa.

Ehanire ya kuma ce ana sa ran za a fara kashi na biyu na rigakafin cutar samfurin Moderna a ranar Litinin mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!