Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi – Ƴan bindiga sun sako kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja

Published

on

Kwmishinan yaɗa Labarai na jihar Neja da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaƙi iskar ƴanci.

Muhammad Sani Idris ya shafe kwanaki hudu a hannun ƴan bindigar bayan sace shi da suka yi har gida.

Da yammacin Alhamis ɗin nan ne kwamishinan ya kuɓuta daga hannun su kamar yadda shugaban karamar hukumar Tarfa Alhaji Ibrahim Mami ya bayyanawa Freedom Radio.

Ya kuma tabbatar da cewa, ba a biya kuɗin fansa domin sakin sa ba, sai dai tun a ranar da ƴan bindigar suka sace shi sun buƙaci a biya wasu kuɗaɗe kimanin miliyan ɗari biyar kafin su sake shi.

Yanzu haka dai an garzaya da kwamishinan zuwa asibiti don duba lafiyar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!