Labarai
Ba za mu yarda a yi amfani da makamai ko ƙwayoyi yayin bikin Maukibi- Ƴan sanda

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta bayyana cewa, ta kammala shirye-shiryenta wajen tabbatar da tsaro yayin gudanar da bikin Maukibin Qadiriyya na bana a yau Asabar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a dare Juma’a nan.
Ta cikin sanarwar, rundunar ta kuma yi gargadin cewa ba za ta yarda a yi amfani da makamai, kokuma ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi da za su iya kawo cikas yayin taron.
You must be logged in to post a comment Login