Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba zamu bude makarantu ba, har sai mun samar da tsarin kare dalibai – Minista

Published

on

Gwamnatin tarraya ta ce ba zata bude makarantun fadin kasar nan ba, har sai an bullo da sabbin tsare-tsare kare dalibai daga kamuwa da cutar Corona.

Karamin ministan Ilimi Chukewuemeka Nwajiuba ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartasawa ta kasa a jiya Labara.

A cewar sa, duk da majalisar wakilai ta bukaci da a bude makarantun kasar nan sannan a baiwa daliban ‘yan-ajin karshen na sakandire damar rubuta  Jarrabawar kammala sakandire ta yammacin Afirka WAEC, ba daidai bane a bude makarantu ko bawa daliban rubuta jarrabawar, ba tare da an bullo da tsare-tsaren kare su daga kamuwa ko yada cutar ba.

Karamin ministan ilimin ya kuma ce, ma’aikatar ilimi ta lura da cewa, akwai hadari babba idan har aka bar dalibai suka koma makarantu yayin da ake tsaka da wannan cuta mai hadarin gaske.

Yana mai cewa, a yanzu haka masu ruwa da tsaki na tsaka da tattaunawa kan yiwuwar bude makarantu ko baiwa dalibai ‘yan-ajin karshe damar rubuta jarrawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!