Kasuwanci
Ba za mu canja tsarin takaita hada-hadar Kudi ba- NFIU
Hukumar kula da harkokin kudi ta Nijeriya ta ce babu gudu ba ja da baya, a tsaren-tsarenta na takaita cirar kudi da ta fitar a farkon watan nan dangane da hada-hadar kudade na Falan gwamnati uku.
Hukumar ta NFIU ta fitar da sanarwar ne a matsayin martani ga ganawar da ta yi da gwamnonin jihohi 36 na kasar da suka nemi ta sake duba na tsanaki akan tsarin.
Kungiyar Gwamnoni ta kasa NGF dai tayi Allah-wadai da umarnin da hukumar ta NFIU ta bayar a baya-bayan nan.
Tun a ranar 5 ga Janairun da muke ciki ne dai Nigerian Financial Intelligence Unit, ta umarci bankunan kasar nan da su daina aiwatar da bukatu na tsabar kudi daga asusun Gwamnati, da kuma biyan kudaden alawus na balaguro, daga ranar 1 ga watan Maris din bana.
You must be logged in to post a comment Login