Labarai
Ba zamu lamunci kalaman batanci ga Kwankwaso ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su daina cin mutunci ko sukar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tana mai cewa duk wanda ya yi hakan zai fuskanci hukunci.
Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnati, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce dole a mutunta Kwankwaso duk da sauyin siyasa, yana mai kira ga magoya baya da su nuna ladabi da kamun kai.
You must be logged in to post a comment Login