Labarai
Ba zamu lamunci karin farashin mai fetur ba – NLC
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce bazata amince da Karin farashin man fetur da akayi daga naira dari da arba’in da takwas da kobo hamsin zuwa naira dari da hamsin da daya da kobo hamsin da shida a kowacce lita.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce abin takaicin bai wuce yadda a ranar biyar ga watan Agustan da ya gabata aka samu Karin farashin mai daga naira dari da arba’in da uku da kobo hamsin zuwa dari da araba’in da takwas da kobo hamsin kan kowacce lita.
Ayuba Wabba ya kuma ce tun a jiya wasu daga cikin gidajen mai da ke Abuja suka fara sayar da man a kan sabon farashin na dari da sittin da daya kan kowacce lita, yana mai cewa Karin yazo a daidai lokacin da yan kasar nan ke cikin halin matsin rayuwa.
Kazalika ya ce baza su goyi bayan wannan Karin man da ake samu akai akai ba wanda a cikin watanni uku an samu Karin sau uku wanda a yanzu yazo daidai da Karin farashin wutar lantarki don haka abin Allah wadai ne.
You must be logged in to post a comment Login