Labarai
Ba zamu soke sakamakon mazaɓun da yara suka kaɗa ƙuri’a ba -KANSIEC
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce, hukumar ba za ta soke sakamakon zaɓukan yankunan da aka samu rahotannin kananun yara suna kaɗa kuri’a ba.
A cewar sa, tun farko hukumar ta shaidawa jam’iyyu cewa su sanar da jamian tsaro a duk lokacin da suka ga ƙananan yara suna kaɗa kuri’a don ɗaukar matakin da ya dace.
Ya ce, zuwa yanzu rahotannin da hukumar ke samu zaɓe na tafiya lami lafiya sai dai ɗan abin da ba a rasaba.
Da aka tambaye shi game da rashin kaɗa ƙuri’a a kan lokaci, ya ce a rahotannin da suka samu kayyakin zaɓe sun isa rumfunan zaɓe a kan lokaci, wurare kaɗan ne aka samu akasi.
Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya kuma ce, hukumar za ta ci gaba da sanya idanu don ganin an kammala zaɓen bisa ƙa’ida.
You must be logged in to post a comment Login