Connect with us

Labarai

Yanzu-yanzu: Gwamna Ganduje ya kaɗa ƙuri’arsa

Published

on

Ku ci gaba da bibiya ana sabinta wannan shafi da sabbin bayanai.
Basheer Sharfadi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Gwamnan ya bi layi har yazo kansa sannan ya kaɗa ƙuri'arsa.

A mazaɓar an ɗauki matakan kariya na wanke hannu da sinadari saboda cutar Korona.

Wakiliyar mu Zahra'u Nasir ta ce, an samu dandazon al'umma a mazaɓar da suka fito domin kaɗa ƙuri'a.

Sai dai ba a samu bayar da tazara a tsakanin juna ba.

Basheer Sharfadi

An fara kawo kayan zaɓe a Bachirawa

Wakiliyar mu Jamila Ado Mai Wuka ta ce, an fara kawo kayan zaɓe a makarantar Firamaren Bachirawa da ke ƙaramar hukumar Ungogo da karfe 9:26.

Basheer Sharfadi

8:56am babu masu zaɓe da malaman zaɓe a Ƙofar Ruwa, Gidan Gawo

A mazaɓar Gidan Gawo da ke Ƙofar Ruwa 'A' mai akwatunan zaɓe guda biyu,da yawan masu zaɓe 1,500 har ƙarfe 8:56 na safe babu kayan zaɓe babu malaman zaɓe, sannan babu masu ƙaɗa ƙuri'a.

Basheer Sharfadi

Ƙarfe 8:25 ba kayan zaɓe ba malaman zaɓe a Ɗandishe

Wakilin mu Hassan Auwal Muhammad da ya ziyarci Ƙofar gidan mai unguwar Ɗandishe da ke ƙarƙashin mazaɓar Ƙofar Ruwa ya ce, babu malaman zaɓe, sannan ba a kawo kayan zaɓe ba.

Mazaɓar na da akwatunan zaɓe huɗu.

Ku kalli hotuna a kasa.

Basheer Sharfadi

Yau Asabar al'ummar jihar Kano ke kaɗa ƙuri'u a zaɓen kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi.

Ana gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Tsagin hamayya na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya ce, ba zai shiga zaɓen ba.

Ita ma a ɓangarenta hukumar zaɓen jihar Kano KANSEIC ta ce zata tabbatar an yi adalci a zaɓen.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano kuwa, ta sanar da dokar taƙaita zirga-zirga tun daga sha biyu na daren Jumu'a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.