Labarai
Ba zan sake tsayawa takara a 2023 ba – Gwamna Masari
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya yi watsi da raɗe -raɗin da ake yi cewa zai ƙara tsayawa takarar neman wani muƙamin siyasa a kakar zaben 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai.
Masari ya ce, matuƙar ya kammala wa’adin sa na biyu ba zai sake tsayawa takarar neman kujerar siyasa ba, sai dai zai goyi bayan matasa masu tasowa da su tashi tsaye don neman muƙaman siyasa da shugabancin jama’a.
“Ba zan yi takarar kowane muƙami ba a cikin jam’iyya ko a gwamnati, na kasance shugaban majalisar dokoki ta ƙasa don haka bana sake sha’awar komawa cikin ta” in ji Masari.
“A cikin jam’iyyar APC ma ni ne mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa shiyyar Arewa don haka wane matsayi zan ƙara nema a jam’iyyar?” A cewar Masari.
Gwamnan Katsinan ya ce, lokaci ya yi da za a ƙyale matasa masu tasowa su taka ta su rawar.
You must be logged in to post a comment Login