Connect with us

Labarai

Babban Hafsan Tsaro ya tura Runduna ta musamman zuwa Kwara da Neja

Published

on

Babban Hafsan Tsaron kasar nan , Janar Olufemi Oluyede, ya ce za a tura rundunar sojoji ta musamman zuwa Jihar Kwara da wasu sassan Jihar Neja domin magance Kalubalen tsaro.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin gabatar da bitar kasafin kuɗin 2025 da kuma ƙudirin kasafin 2026 a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai.

 

Janar Oluyede ya ce sojoji sun samu nasarori wajen yaƙar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, sai dai domin ɗorewar zaman lafiya dole ne a ƙara ƙarfafa rundunar ‘yansanda da Hukumar tsaro ta  NSCDC domin su riƙe yankunan da aka ƙwato.

 

Ya kuma ce an riga an tura runduna ta musamman zuwa jihohin Benuwe da Filato, sannan za a ƙaddamar da wata sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Savannah Shield domin aiki a Kwara da wasu sassan jihar  Neja.

 

Babban hafsan ya ƙara da cewa sojoji na fuskantar ƙarancin ma’aikata, don haka akwai buƙatar ƙarin haɗin kai da isasshen tallafi domin inganta tsaro a faɗin ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!