Labarai
Babban Jojin Najeriya ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa
Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya lashi takobin yaki da duk wani nau’i na cin hanci da rashawa da ke cikin hukumar shari’ar kasar nan.
Tanko Muhammad ya shaida hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da shi jiya a Abuja.
Ya kuma bayyana hukumar shari’ar kasar nan a matsayin wadda ta yi zarra a nahiyar Afirka la’akari da irin horon da jami’an ke samu ta fannoni daban-daban, inda ya yi fatan nan gaba za ta kere sa’a a duniya.
Tanko Muhammad ya bukaci ‘yan Jarida su taimakawa kokarinsa ta hanyar tona asirin masu cin hanci da rashawa a cikin hukumomin shari’a a ko ina su ke, kasancewar ba duka aka taru aka zama daya ba.
Babban Jojin ya ce kamar yadda a ke samun wasu ‘yan Najeriya da aikata laifukan cin hanci da rashawa, haka ma wasu alkalai ke aikata hakan, dalilin kenan da ya sa ya zama wajibi a bankado su.