Labarai
Babban layin Lantarki na Najeriya ya sake faduwa
Ofishin kula da ke kula da babban layin wutar lantarki na kasar nan, ya ce layin ya sake sauka a yau Laraba da misalin karfe 2 da minti tara na rana.
Ofishin ya bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Haka kuma ya kara da cewa, tuni aka fara kokarin dawo da layin bakin aiki.
Rahotonni sun bayyana cewa, karo na goma sha biyu kenan a shekarar nan ta 2024 da muke ciki.
Sai dai Ofishin, ya nemi afuwar al’ummar kasar nan ya na mai cewa tuni aka dukufa don dawo da wutar.
You must be logged in to post a comment Login