Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tsaro

Babban Sufeton Ƴan sanda ya turo samar da jirgi mai sauka Ungulu a Kano yayin zaɓe

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, babban Sifeton yan sanda Usman Alkali Baba, ya sake turo jirgin sama mai saukar Ungulu wanda ke dauke da na’urorin daukar hotuna da zai rika shawagi a sararin samaniya domin tabbatar da cewa an yi zabe lafiya a yau Asabar.

Mai magana da yawun rundunar na Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.

SP Kiyawa ya kara da cewa , baya ga jirgin saman da babban Sifeton ya aiko, akwai karin jami’an tsaro da karin bindigogi da sauran kayayyakin inganta tsaro domin ganin an yi zabe lafiya an gama lafiya.

Haruna kiyaw ya ce jihar Kano za ta gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali sakamakon matakan tsaro da aka sanya mata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!