Labarai
Babbar daraktar hukumar bada lamuni ta duniya ta ajiye aiki
Babbar daraktan hukumar bada lamuni ta duniya IMF Ms Christine Lagarde ta ajiye aiki.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da Ms Lagarde din ta bayar a shafin internet na hukumar a jiya Talata cewa kafin ajiye aikin sai da ta gana da hukumomin daraktocin IMF daga bisani kuma ta bada takardar ajiye aikin ta da zai fara aiki daga ranar 12 ga watan Satumba mai zuwa.
Akan hakan ne hukumomin darakoticin hukumar bada lamunin suka sanar da cewa Mr David Lipton zai rike mukamin mai rikon babban manajin daraktan IMF kafin a sanar da wanda zai maye gurbin ta.
Ms Christine ta ce biyo bayan zabar ta da aka yi a matsayin shugabar babbn bankin tarayyar Turai, ya zama wajibi don cigaban hukumar bada lamuni ta duniya na ajiye aiki na