Kiwon Lafiya
Abdulrashid Maina:Babbar kotun tarayya ta yi watsi da bukatar Ministan Shari’a
Babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya ta ki amincewa bukatar da Atoni Janar kuma ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi, na dakatar da yunkurin majalisar Dattijai na gudanar da binciken yadda aka maida Abdulrashid Maina, tsohon shugaban kwamitin kar-ta-kwana wajen gyaran harkokin fansho bakin aiki.
Mai Shari’a Binta Nyako ta bada umarnin aikewa majalisun Dokokin kasar nan bukatar kare kansu kan kudurin na su.
Ministan Shari’ar ya kalubalanci yunkurin kwamitin majalisar Dattijan kan ayyukan gwamnati, harkokin cikin gida da kua yaki da cin hanci, na nazartar yadda aka maida Abdulrashid Maina bakin aiki , inda ya bukaci kotun ta duba shin ko majalisar da ikon gudanar da binciken.
Abubakar Malami na da ra’ayin cewa sashe na 88(1) da (2) na kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi cikakken bayani kan ikon majalisun Dokokin kasar nan ke da shi kan wannan batu bayan da ya bada iyaka