Labarai
Babu ƴan kallo a wasan da Kano Pillars za ta fafata da Barau FC.

Ƙunguyar kwallon ƙafa ta Barau FC ta ƙayyade adadin mutanen da za su shiga filin wasa na Sani Abacha dake Kano a wasanta da Kano Pillars na yau.
Barau FC wacce ita za ta karbi bakuncin Kano Pillars, ta ƙididdige adadadim mutane 120, da suka haɗa da ƴan wasa, da ƴan jarida da alƙalan wasa, da kuma jami’an Hukumar wasanni ta jihar da na NPFL.
Barau ta kayyade wa kanta shiga da mutane 30 har ƴan wasa, Kano Pillars ma haka, sai ƴan jarida mutum 10, sauran jami’an tsaro da na Hukumomin wasan kuma mutum 50.
Wannan matakin ya biyo bayan wata hatsaniya da ta kaure a filin a wasan da Pillars ta buga da Shooting Stars a Lahadin da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login