Labarai
Babu direban adaidaita sahun da zai ci gaba da aiki ba tare da sabunta lamba ba – Baffa Babba
Hukumar KAROTA ta jihar ta ce, babu wani matuƙin baburin dadidaita sahu da zai ci gaba da yin sufuri akan titi ba tare da ya sabunta lambarsa ba, a bana.
Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka d Hantsi na nan Freedom Radio.
Shirin ya mayar da hanakali kan batun tsarin ayyukan hukumomin da ke kula da harkokin sufuri a ƙasarnan musamman a jihar Kano, domin sanin hurumin kowace hukuma da nufin kaucewa cin karo da juna a wajen gudanar da aiki.
Baffa Babba Danagundi ya ce “sabunta lambar na cikin tsarin dokar hukumar KAROTA wadda ta ce, a kowacce shekara ya zama wajibi kowanne direban Babur mai kafa uku ya sabunta ta”.
“Ta hanyar sabunta lambar ne ake iya gane adadin wadanda suka mallaki baburin a kowacce shekara, da ma bada dama wajen binciko masu fakewa da baburin suna aikata laifukan da suka saɓawa doka” a cewar Baffa.
Ya kuma ce, suna sane da yadda ake samun wasu babura masu lamba iri ɗaya wanda kuma ya saɓa doka.
Da yake bayani kan matakin hukumar na hana manyan motoci shiga wasu titina anan Kan, Baffa Babba Danagundi ya ce, tuni shiri yayi nisa na fara sanya turakun hana motoci shiga da fice guraren da za su iya haifar da illa ga al’ummar cikin sa.
Wannan dai na zuwa yayin da ake ci gaba da ganin ayyukan jami’an hukumomin na cin karo da juna musamman ma wadanda suke gudanar da ayyukan su akan titi.
You must be logged in to post a comment Login