Kasuwanci
Babu hannu na a musgunawa ‘yan kasuwannin Kwari da Sabon Gari – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce bata da hannu cikin uzzurawar da shuwagabannin hukumomin kasuwar Kantin Kwari da ta Sabon Gari ke yiwa ‘yan kasuwannin.
Mai baiwa gwamnan Kano shawara akan harkar kasuwanci Mahmud Sani Madakin Gini ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da Freedom Radio.
Madakin Gini ya ce ko kadan babu ruwan gwamnatin Kano cikin karbar kudade dubu guda-guda a hannun ‘yan kasuwar Kantin Kwari ba bisa ka’ida ba.
Dangane da batun tilastawa ‘yan kasuwar Sabon Gari siyan na’urar Sola ‘yar gata kuwa, Madakin Gini ya ce ba da sanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kayi haka ba.
Idan zaku iya tunawa a kwanakin baya hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta ce ta gano wasu gine-ginen kofa da shugaban hukumar kasuwar Kantin Kwari yayi ba bisa ka’ida ba, kuma tana cigaba da bincike akai.
Karin labarai:
Ba ma bukatar sanya Solar -‘yan kasuwar Sabon gari
Ana zargin hukumar kasuwar Kantin Kwari da zama saniyar tatsa – Anti Kwarrafshan
You must be logged in to post a comment Login