Connect with us

Kasuwanci

Babu hannu na a musgunawa ‘yan kasuwannin Kwari da Sabon Gari – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce bata da hannu cikin uzzurawar da shuwagabannin hukumomin kasuwar Kantin Kwari da ta Sabon Gari ke yiwa ‘yan kasuwannin.

Mai baiwa gwamnan Kano shawara akan harkar kasuwanci Mahmud Sani Madakin Gini ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da Freedom Radio.

Madakin Gini ya ce ko kadan babu ruwan gwamnatin Kano cikin karbar kudade dubu guda-guda a hannun ‘yan kasuwar Kantin Kwari ba bisa ka’ida ba.

Dangane da batun tilastawa ‘yan kasuwar Sabon Gari siyan na’urar Sola ‘yar gata kuwa, Madakin Gini ya ce ba da sanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kayi haka ba.

Idan zaku iya tunawa a kwanakin baya hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta ce ta gano wasu gine-ginen kofa da shugaban hukumar kasuwar Kantin Kwari yayi ba bisa ka’ida ba, kuma tana cigaba da bincike akai.

Karin labarai:

Ba ma bukatar sanya Solar -‘yan kasuwar Sabon gari

Ana zargin hukumar kasuwar Kantin Kwari da zama saniyar tatsa – Anti Kwarrafshan

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Kasuwanci

Yiwa kananan ‘yan kasuwa rijista zai bunkasa kasuwancin su-CAC

Published

on

Hukumar yiwa kamfanoni Rijista ta kasa (CAC) ta ce yin rijistar kasuwanci ga kananan ‘yan kasuwa zai sa kasuwancin su ya inganta tare da samun riba mai yawa.

Babban magatakarda a hukumar ta Corporate Affairs Commission wato (CAC), Alhaji Garba Abubakar ne ya bayyana hakan ya yin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a hukumar.

Garba Abubakar ya kuma ce yin rijistar ga kananan ‘yan kasuwar zai sanya banku su rinka basu rancen kudade don inganta kasuwancin su.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a hukumar da suka halarci taron sun bayyana jindadin su game da ayyukanta, musamman ta yadda ake yiwa dan kasuwa ko mai kamfani rijistar kasuwancin sa a cikin Awa guda.

A yayain taron dai an baiwa mutanan da suka halarci taron damar bayar da shawara ko shigar da korafi kan yadda za’a kara inganta aikin hukumar.

Continue Reading

KannyWood

Cibiyar horas da harkar fim ta bullo da hanyoyin bunkasa sana’ar

Published

on

Shugaban sashen horas da dabarun shirya fina-finai, Alhaji Musa Gambo, ya nemi kungiyoyin masu gudanar da sana’ar fim su rinka tura mambobinsu wuararen samun horo domin ciyar da bangaren gaba a Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a bikin yaye daliban makarantar da samu horo kan yadda ake shirya fina-finai.

Alhaji Musa Gambo ya ja hankalin daliban da suyi amfani da horon da suka samu wajen tsara fina-finan da zasu dace da al’adun Hausawa da ma sauran al’adun Najeriya.

Karin Labarai:

Halin da ake ciki a Kannywood a wannan mako

Muhimman abubuwan dake faruwa yanzu haka a Kannywood

A cewar sa, gwamnatin jihar Kano na kokartawa don ganin ta bunkasa harkar fina-finai da ma al’adun Hausawa a jihar da ma kasa baki daya.

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa daga cikin manyan bakin da suka hallarci taron akwai shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakalla.

Continue Reading

Kasuwanci

Wasu ‘yan kasuwar Sabon gari sun koka kan yunkurin Uba Zubairu

Published

on

Wasu ‘yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwancin a filin parking na Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari anan Kano, sun koka dangane da yunkurin tashin su da suka ce shugabannin kasuwar na kokarin yi.

‘Yan kasuwar dai sun ce shugabannin kasuwar karkashin Uba Zubairu Yakasai, ya aike da wani mutum rike da abar magana yana cewa su tashi daga kasuwar nan da mako daya.

Sun kuma shaidawa Freedom Rediyo cewar shakka babu za su fada cikin mawuyacin hali idan aka tashe su.

Alhaji Abba Muhammad na zaman daya daga cikin shugabannin leburorin da suke aiki a wajen, ya bayyana cewa kasancewar dayawa daga cikin su masu kananan karfi ne, idan har aka tashe su basu san inda za su zauna don gudanar da kasuwancin su ba.

Da yake jawabi, daraktan mulki na kasuwar Muhammad Bashir Abdul Durumin Iya, ya ce Gwamnatin jihar Kano ce ta bayar da umarnin tashin su don za tayi amfani da wajen.

‘Yan kasuwar sun bayyana mana kafar mu cewar, mutanen dake kasuwanci a wajen sun doshi sama da dubu uku.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,535 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!