Labarai
Babu hannuna a ɗaukaka ƙara – Malam Abduljabbar
Wasu daga cikin ɗaliban Malam Abduljabbar Nasir Kabara sun barranta kansu da matakin daukaka ƙara kan hukuncin da aka yi masa a baya.
Wannan dai ya biyo bayan yadda wasu daga cikin ɗaliban nasa suke ƙoƙarin ɗaukaka ƙara kan shari’ar da aka yiwa Malamin.
Martanin nasu na zuwa ne bayan samun rubutacciyar takarda da suka yi daga hannun malami Abduljabbar, inda yake barranta kansa da matakin da wasu ɗaliban nasa ke kokarin ɗauka.
Malam Saifullahi Satatima ɗaya na daga cikin ɗaliba Malam Abduljabbar, ya shidawa Freedom Radio cewa “Mun samu wata takarda daga hannu Malam mai ɗauke da sa hannunsa da yake nesanta kansa daga matakin wasu ɗaliban na ɗaukaka ƙara”.
“kuma wannan takarda an sanya ta a wani shafin internet na Facebook wanda ya kasance ɗaya daga cikin shafukan da Malam yake bada saƙo a cikinsa, don haka babu hannun malam a wannan mataki” a cewar Malam Saifullahi.
Malam Saifullahi Satatima wanda ya kasance ɗalibi ga malam Abduljabbar, kuma ya kasance limamin masallacin juma’a na Jami’a Rasulullah a Kano.
Idan za a iya tunawa wasu ɗaliban Malam Kabara sun buƙaci babbar kotun jihar Kano ta amince su ƙalubalanci hukuncin kotun Ƙofar Kudu da ta zartar masa.
You must be logged in to post a comment Login