Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu hujja cewa jami’an tsaron Najeriya sun kashe masu zanga-zangar ENDSARS – Amurka

Published

on

Sashen kula da harkokin kasashen waje na Amurka ya ce babu wata kwa-kw-kwarar hujjar jami’an tsaron Najeriya sun kashe masu zanga-zangar ENDSARS a ranar 20 ga watan Oktoban bara a mashigar Leki dake Legas.

Bayanin hakan na cikin wani rahoto da sashen ya wallafa da hadin gwiwar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa.

Sai dai rahoton ya nuna karara, yanda jami’an tsaro suka ci zarafin masu zanga-zangar.

Itama babbar jami’a a ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing ta ce tabarbarewar da al’amuran tsaro sukayi a kasar nan, na zama wani abin damuwa ga Birtaniya.

Ta ce Birtaniya za ta taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!