ilimi
Babu wasu kuɗi da gwamnatin tarayya ta biya mu zuwa yanzu – ASUU
Ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta musanta batun gwamnatin tarayya na cewar ta bai wa ƙungiyar naira Biliyan 52.
Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kano da ya ƙunshi hadakar jami’o’i bakwai, Kwamred Abdulƙadir Muhammad ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba.
Abdulƙadir Muhammad ya ce, kalaman na gwamnatin tarayya na biyan ƙungiyar kuɗaɗe ba dai dai bane, haka zalika wata manufa ce ta ɓata sunan ƙungiyar da ƴa ƴanta.
“Mun samu labarin yadda ministan ƙwadago da samar da aikin yi Chris Ngige yana cewa gwamnati ta bai wa ƙungiyar mu Naira miliyan 52, to wannan batu ba daidai ba ne ba’a kyauta mana ba, kuma an yi ne don ɗauke hankalin al’umma”.
Ya ci gaba da cewa “Duk kuɗaɗen da yake naga ba ƙungiyar ASUU aka bai wa makarantun jami’o’i aka bai wa domin su magance matsalolin su”.
Ƙungiyar ta kuma bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da su ɗauki matakin kawo ƙarshen hare haren ‘yan Bindiga da masu garkuwa da mutane ba gaira ba dalili, tare da kaucewa batun ƙarin kuɗin haraji da cire tallafin Man Fetur.
You must be logged in to post a comment Login