Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu wasu mutane ko kungiyoyi da muka dauka a matsayin masu ba da shawara kan daukar ma’aikata a hukumar – INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta musanta daukar mutane ko wasu kungiyoyi a matsayin masu ba da shawara kan daukar ma’aikata a hukumar.

INEC ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugaban sashin wayar da kan masu zabe Festus Okoye ya sanyawa hannu.

Okoye ya bukaci jama’a da su kai rahoto ga hukumomin tsaro, kan mutane ko kuma kungiyar da ke ikirarin cewa tana tuntubar  hukumar kan daukar ma’aikata.

A cewar sanarwar wasu ‘yan damfara da ke ikirarin yi wa hukumar aiki a kan daukar ma’aikata sun kai ga rufe tambarin INEC sannan suka fara neman masu neman aiki a hukumar.

Ta cikin sanarwar INEC ta bukaci jama’a da guji fadawa hannun masu damfara da suke bude shafukan Internet da sunan hukumar ga masu neman aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!