Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Mun zaftare albashin watan Maris na kusoshin gwamnati – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta zaftare albashin shugabannin da ke rike da madafun iko a gwamnatin da kaso hamsin cikin dari na watan Maris da ya gabata.

Hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar.

A cewar sanarwar matakin ya zama wajibi sakamakon yadda gwamnatin ta karbi Kason ta daga hannun gwamnatin tarayya wanda kuma ya zamo mafi kankanta.

A cewar sanarwar an zaftare kason shugabannin ne tun daga matakin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da sauran masu rike da mukaman siyasa.

Wannan dai ya biyo bayan yadda gwamnatin ta ce bazata iya biyan mafi karancin albashi na dubu talatin a watan na Maris ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!