Labarai
Babu zirga-zirgar ababen hawa a yankunan da za a yi zaɓe- CP Bakori

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewar babu zirga-zirgar ababen hawa a kananan hukumomin Bagwai da Shanoni da kuma Ghari, tun daga karfe shida na safiyar Asabar zuwa uku na Yamma sakamakon zabukan cike gurbi na ‘yan majalisun dokokin jihar Kano da za a gabatar.
Kwamishinan yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio, jim kadan bayan kammala taro na musamman da masu ruwa da tsaki kan zabukan da za a gabatar.
Kwamishina Ibrahim Adamu Bakori, ya kuma ja kunnen duk wanda yasan ba zabe zai ba daya guji zuwa yankunan da za a gudanar da zabukan dan kuwa idan suka kama mutum doka za tai aiki a kansa.
Da ya ke nasa jawabi, shugaban hukumar zabe ta kasa INEC reshen Jihar Kano Ambassador Abdu A Zango ya ce, sun shirya tsaf dan gudanar da zabukan.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a gudanar da zabukan cike gurbin a kananan hukumomin Bagwai da Shanono da kuma karamar hukumar Gari.
You must be logged in to post a comment Login