Connect with us

Labarai

Da dumi –dumi : Ganduje zai bude makarantun boko a Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da a bude makarantun boko a ranar 10 ga watan Agusta don rubuta jarrabawar kammala sakandire a sassan jihar nan a bana.

Kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sanusi Kiru ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka yi a yau Litinin.

Muhammad Sanusi Kiru ya umarci dukkanin shugabannin makarantu su tsara wajen karbar dalibai dake makarantun kwana a ranar 9 ga wannan watan na Agusta, don fara karatu gadan-gadan.

A dai watan Maris ne gwamnatin jihar Kano ta garkame makarantun jihar don kare dalibai daga kamu daga cutar COVID -19.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!