Connect with us

Jigawa

Badaru ya bukaci hukumomin shari’a da su kasan ce masu aikata gaskiya

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci hukumomin shari’a da su kasan ce masu aikata gaskiya a dukkanin ayyukan su.

Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da sabbin mambobin hukumar shar’a a jihar da ya gudana a ranar Alhamis 16 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce nade-naden sun samo asali ne bisa cancanta da jajircewar su wajen yiwa jihar hidima.

Kwamishinan shari’a na jihar Dakta Musa Adamu Aliyu ne ya rantsar da su.
Wadanda aka rantsar sun hadar da Dakta Abdulkadir Saleh kazaure da Barrister Jamila Faruk.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!