Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin Maita: Yan sanda a jihar Adamawa sun tabbatar da mutuwar mutane 7

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wasu mutane bakwai sakamakon zargin su da Maita a Kauyen ‘Dasin ‘Kwate dake karamar hukumar Fofore a jihar.

Mai Magana da yawun rundunar DSP Sulaiman Yahya Guroje ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yammacin ranar Alhamus 16 ga watan Satumbar shekarar 2021.

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kashe dan Sanata Na-Allah a Kaduna

DSP Guroje ya ce lamarin ya faru a ranar Larabar 15 ga watan, bayan da mutanen Kauyen na ‘Dasin ‘Kwate suka zargi mutanan da Maita wanda hakan yasa suka kashe su.

Haka zalika DSP Sulaiman ya ce bayan faruwar lamarin mutanan kauyen sun gude zuwa wasu yankunan a jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, ta baza jami’an ta lungu da sako na karamar hukumar ta Fofore da kewayenta domin lalubo wadan da suka aikata laifin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!