Jigawa
Badaru ya gudanar da dashen bishiyoyi a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta fara dashen bishiyoyi miliyan biyu da dubu dari biyar domin kaucewa daga kwararowar Hamada a fadin jihar.
Gwamnan jihar Muhammadu Badaru Abubakar ya kaddamar da fara dashen bishiyoyi a garin Andaza dake karamar hukumar Kiyawa.
Bishiyoyin sun hada da Turare dubu dari takwas, da Darbejiya dubu dari biyar da arbain da biyar sai kuma bishiyar Zogale dubu dari da kuma bishiyar Dorawa dubu hamsin da biyar.
Sauran sun hada bishiyar Kuka dubu ashirin da bishiyar Madachi dubu ashirin da kuma bishiyar Kashu da sauran su.
Gwamna Badaru ya kara da cewa gwamnatin sa ta dasa bishiyoyin ne kimanin miliyan goma cikin shekaru hudun mulkin sa.
Ya kara da cewa jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi masu fama da barazanar hamada
You must be logged in to post a comment Login