Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Badaru ya gudanar da dashen bishiyoyi a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara dashen bishiyoyi miliyan biyu da dubu dari biyar domin kaucewa daga kwararowar Hamada a fadin jihar.

Gwamnan jihar Muhammadu Badaru Abubakar ya kaddamar da fara dashen bishiyoyi a garin Andaza dake karamar hukumar  Kiyawa.

Bishiyoyin sun hada da Turare dubu dari takwas, da Darbejiya dubu dari biyar da arbain da biyar sai kuma bishiyar Zogale dubu dari da kuma bishiyar Dorawa dubu hamsin da biyar.

Sauran sun hada bishiyar Kuka dubu ashirin da bishiyar Madachi dubu ashirin da kuma bishiyar Kashu da sauran su.

Gwamna Badaru ya kara da cewa gwamnatin sa ta dasa bishiyoyin ne  kimanin miliyan goma cikin shekaru hudun mulkin sa.

Ya kara da cewa jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi masu fama da barazanar hamada

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!