Labarai
Bai kamata gwamnatin Najeriya taki amincewa da bukatun majalisar dattawa ba – Ahmed Lawan
Majalisar Dattijai ta kasa ta ce, fadar shugaban kasa bata karbi shawarwarin da suka kamata ba, na soke wasu daga cikin bukatun majalisar na neman shugaban kasa Muhammad Buhari ya sahale mata aiwatar da wasu ayyuka.
Shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan ne ya bayyana hakan, yayin taron jin ra’ayin al’umma da kwamitin majalisar bangaren kiwon lafiya ya gudanar, kan wasu kudurori uku da kwamitin ya bukata.
Kwamitin ya ce ya bukaci a samar da asibiti na musamman a garin Suleja, dake jihar Niger da kuma Jami’ar koyar da harkokin lafiya ta gwamnatin tarayya a jihar Ogun sai kuma asibitin kashi da za’a samar a garin kuta dake jihar Niger.
Ahmad Lawan, ya ce kin amincewa a gudanar da ayyukan da fadar ta shugaban kasa ta yi ba karamin koma baya zai kawo ba a sha’anin lafiya a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login