Labarai
Bai kamata gwamnatin Shugaba Tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur. – Sarkin Kano Sunusi II

Sarkin Kano na 16 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin kasa CBN, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa, bai kamata gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur.
Sarkin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a birnin tarayya Abuja a Talatar makon nan, a taron Oxford Global Think Tank Leadership da kuma ƙaddamar da wani littafi.
Haka kuma, Sarki Muhammadu Sanusi ll, ya kara da cewa cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Sarkin, ya kuma yaba wa gwamnatin shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan gyare-gyare ba za su yi tasiri ba sai an haɗa su da tsari mai kyau na kashe kuɗi da gaskiya a cikin gudanar da al’amuran gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login