Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Published

on

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawar sirri da mai martaba Sarkin Kano na 14 Malam Sanusi Lamido Sanusi a fadar mulki ta Villa a daren Alhamis din makon nan.

Rahotonni sun bayyana cewa, Sanusi Lamido, ya isa fadar shugaban kasar sa’o’i kadan bayan da shugaba Tinubu ya kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa, a taron da ya samu halartar gwamnoni da dama da kuma manyan mataimakan shugaban kasa.

Yanzu haka dai, alkiblar tattalin arzikin gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi dai-dai da tunanin Sarki Muhammadu Sunusi II, wanda tsohon gwamnan babban bankin CBN ne.

Basaraken wanda masanin tattalin arziki ne, ya kuma kasance mai rajin kawo karshen biyan tallafin man fetur, manufar da shugaba Tinubu ya aiwatar tun ranar da ya sha rantsuwar kama aiki.

Wannan dai shi ne karon farko da Sarki Muhammadu Sunusi ke ganawa da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a fadar ta Villa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!