Labarai
Bama goyan bayan yin zanga-zanga a Kano – JONAPWD
Gamayyar kungiyoyin masu bukata ta musamman a Kano sun nesanta kansu daga cikin mutanan dake yunkurin shirya zanga-zanga kan jinkirin da aka samu na samar da hukumar masu bukata ta musamman da gwamnatin jihar tai alkawarin yi.
Abdurrahman Ubah Daushe shugaban kungiyar masu lalurar laka ta jihar Kano ne yai magana a madadin gamayyar kungiyoyin masu bukata ta musamman din.
Ya kuma ce suna sane kan yadda shirye-shirye sukai nisa na yunkurin samar da hukumar da gwamnatin ta Kano ke yi.
Ya kuma ce gwamnatin ta Kano na kokarin yi musu dukkan abin da suka bukata a wannan lokaci.
Abdurrahman ya kuma zargi hadakar kungiyoyin fararan hula a nan Kani wato KCSF da yunkurin shirya zanga zanga a kai wanda su kuma basu da hannu a ciki.
A ranar laraba 1 ga watan Janairun 2025 ne dai gamayyar kungiyoyin suka gabatar da taron manema labarai inda suka bukaci gwamnatin ta Kano da ta gaggauta samar da hukumar ta masu bukata ta musamman kamar yadda ta alkawarta.
A cikin wata sanarwa da hadakar kungiyoyin suka sanyawa hannu kan nuna rashin goyan bayan su a kwai sa hannun shugaban kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa reshen jihar Kano Musa Muhammad Shaga, dana kungiyar masu lalurar Laka Abdurrahman Ubah Daushe, dana kungiyar masu lalurar gani Musa Muhammad Kura da kuma Yahaya A Yahaya shugaban kungiyar masu bukata ta musamman a nan Kano da sa hannun Da’u Sa’idu shugaban kungiyar masu lalurar Kuturta sai kuma Hajiya Mariya shugabar kungiyar masu lalurar zabiya.
You must be logged in to post a comment Login