Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ban hana ƴan jarida ɗaukar hoton yi min riga-kafi ba – Gwamna Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya musanta raɗe-raɗin cewa ya hana ƴan jarida ɗaukar hoton sa a lokacin da ake masa allurar riga-kafin Korona.

Gwamnan ya musanta hakan ne ta bakin mai taimaka masa kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim cikin zantawar sa da Freedom Radio.

A cewar sa, waɗanda aka hana ɗauka ba ƴan jarida ba ne, mutane ne da ba su da shaidar aiki.

Abubakar Aminu ya ƙara da cewa, wakilan kafafen yaɗa labarai na rediyo da talabijin duka sun ɗauki hotuna da bidiyon Gwamnan a lokacin da ake masa allurar.

A ranar Alhamis ne aka yiwa Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje allurar riga-kafin ta Korona tare da wasu jami’an Gwamnatin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!