Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ban yi na nadamar barin Real-Madrid ba – Gareth Bale

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Gareth Bale, ya ce baya nadamar barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Bale ya bayyana hakan ne a lokacin da ya koma tsohuwar kungiyar sa ta Tottenham da ke kasar Ingila.
Bale ya ce duk da lokacin da ya na wasa a Real Madrid ya samu kwarewa sosai, amma bai yi nadamar barin ta ba.
Gareth Bale, ya koma tsohuwar kungiyar sa ta Tottenham a watan Satumbar da muke ciki, bayan ya kwashe shekaru 7 a kungiyar Real Madrid dake kasar Spaniya.
Bale ya zura kwallaye da dama a kungiyar ta Madrid, ya kuma lashe kofin zakarun Turai wato Champion League guda hudu, da kofuna daban-daban da ya taimakawa kungiyar ta Madrid ta dauka.
A kakar wasanni da ta gabata ta shekarar 2019/2020, mai horas da kungiyar ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya sanya Bale a wasanni hudu kacal, wanda hakan ne a ke ganin ya tilastawa dan wasan sauya sheka zuwa tsohuwar kungiyar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!