Kiwon Lafiya
Babban bankin Najeriya ya yi barazanar korar shugabannin bankunan da suka gaza wallafa rahoton su na karshen shekara
Babban bankin Najeriya ya yi barazanar korar shugabannin bankunan da suka gaza wallafa rahoton su na karshen shekara cikin watanni 12 bayan karewar shekarar, da kuma shugaban hukumar gudanarwar sa daga bakin aiki baki daya.
Wannan umarni na kunshe cikin jadawalin tsarin bayar da bashi, da kuma yadda za yi kasuwanci da kasashen ketare na shekarar 2018/2019 da babban bankin ya fitar da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya sanyawa hannu.
Tsarin jadawalin ya da ce da dokar manufofin kafa bankuna da sauran hukumomin kudi na 1991 wanda ya bukaci bankuna su dinga wallafa bayanan binciken kudin sa da kuma halin da bankin ke ciki a wasu daga cikin manyan jaridun kasar nan domin mutane su fadaka.
A cewar babban bankin hakan zai taimaka wajen dabbaka bibiyar halin da bankuna ke ciki a kasar nan, inda kuma babban bankin ya umarci dukkanin bankunan da sauran hukumomin kudi da su riki ranar 31 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar karshe ta wallafa baya nan.