Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Babban bankin Najeriya ya yi barazanar korar shugabannin bankunan da suka gaza wallafa rahoton su na karshen shekara

Published

on

Babban bankin Najeriya ya yi barazanar korar shugabannin bankunan da suka gaza wallafa rahoton su na karshen shekara  cikin watanni 12 bayan karewar shekarar, da kuma shugaban hukumar gudanarwar sa daga bakin aiki baki daya.

Wannan umarni na kunshe cikin jadawalin tsarin bayar da bashi, da kuma yadda za yi kasuwanci da kasashen ketare na shekarar 2018/2019 da babban bankin ya fitar da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya sanyawa hannu.

Tsarin jadawalin ya da ce da dokar manufofin kafa bankuna da sauran hukumomin kudi na 1991 wanda ya bukaci bankuna su dinga wallafa bayanan binciken kudin sa da kuma halin da bankin ke ciki a wasu daga cikin manyan jaridun kasar nan domin mutane su fadaka.

A cewar babban bankin hakan zai taimaka wajen dabbaka bibiyar halin da bankuna ke ciki a kasar nan, inda kuma babban bankin ya umarci dukkanin bankunan da sauran hukumomin kudi da su riki ranar 31 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar karshe ta wallafa baya nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!