Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Bankin CBN ya saki dala miliyan 100 a kasuwar musayar kudaden ketare

Published

on

Babban bankin Najeriya CBN, ya ce; ya saki dala miliyan 100 a kasuwar musayar kudaden ketare.

A cewar bankin na CBN hakan na zuwa ne awanni 24 bayan tunkudo dala miliyan 210 a ranar Larabar da ta gabata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun bankin Isaac Okorafor.

Isaac Okorafor ta cikin sanarwar dai ya kuma ce an tunkudo kudin musayar ne domin saukakawa al’ummar kasar nan da ke fita ketare domin gudanar da wasu muhimman bukatun da suka wajaba a kansu musamman maniyyatan aikin Hajji bana.

Bankin na CBN a sanarwar ya kara da cewa zai ci gaba da tunkudo dala kasuwar musaya domin dakile karancinsa. Sai dai ya ce zai sanya ido sosai domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai suka amfana da kudin musayar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!