Connect with us

Kiwon Lafiya

A yau ake sa ran shugabannin PDP da suka sauya sheka zuwa APC zasu gana da shugaba Buhari

Published

on

A yau Litinin ne a ke sa ran shugabannin ‘ya yan Sabuwar PDP da suka sauya Sheka zuwa jam’iyyar APC za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Shugaban tawagar Alhaji Kawu Baraje ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Ilorin jihar Kwara, ya ce za su gana da shugaban kasar ne bayan sun tattauna da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

 

Ya kuma ce yana sa ran a karshen ganawar su da shugaban kasar da kuma mataimakin sa, jam’iyyar APC za ta kara samun karfi, za ta kuma kara hada kanta domin amfanuwar al’ummar kasar nan baki daya.

 

Ya kuma ce matakin da kungiyar ta su zata dauka na karshe zai zo ne bayan zaman na su da shugaban kasar.

 

A baya dai mambobin Sabuwar jam’iyyar PDP da su ka koma jam’iyyar ta APC sun baiwa shugabancin jam’iyyar APC waa’din mako guda da su share musu kukan su

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!