Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bankin musulunci zai samar da wajen adana Madara 200 a Kano

Published

on

Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano, da Babban Bankin Musulunci ke daukar nauyi , ya yi alkawarin kashe dalar Amurka Miliyan tara(09),  don kafa Matattarar Madara guda 200, a jiha a tsahon shekaru biyar masu zuwa .

Babban jami’in gudanarwa na aikin Malam Ibrahim Garba , ne ya bayyana haka a jawabin sa na bikin ranar Madara ta duniya, wanda ya kara dacewa shirye shirye sunyi nisa na gina rumbun adana Madarar guda 40, duk shekara wanda za a fara daga wannan shekarar.

Malam Ibrahim Garba Muhammad, a cewar takardar da babban jami’in yada labaran gudanar da aikin Ameen Kabir Yassar , ya sakawa hannu, ya ce kowanne rumbun Adana madarar zai samu famfon Tuka Tuka mai amfani da hasken rana , da zai Adana Madara Lita dubu ashirin a cikin Tanki.

Malam Ibrahim Garba Muhammad, ya kara da cewar za kuma a bada horo na musamman ga masu samar da madara kan yadda zasu Adana madarar cikin yanayi mai kyau da tsafta wanda kawo yanzu haka kungiyoyi 40 na masu samar da Madarar karkashin kungiyar “Fura da Nono Cooperative Groups Ltd” aka ware don baiwa wannan horo na taimako.

Labarai masu alaka.

Zamu tallafawa manoma da irin shuka a jihohi goma sha uku-INCRISAT

Kungiyar manoma ta AFAN ta koka kan bada bashi na Noma

Ya ce shirin zai bada tallafin ma’adanar Madara mai sanyi dake amfani da hasken wutar Lantarki, kayan gwaji da kuma mazubin Madarar.Tare da maida hankali wajen yin allura da bayen Shanu , don bunkasa lafiyar Shanun da samar da madara mai inganci da tsafta, a gefe daya kuma tare da samar da kyakyawan yanayi ga masu saida madara musamman ma Matan Fulani , na tsafta da karin kudin shiga cikin yanayi na Zamani.

Babban jami’in , yace burin tsarin shi ne samar da madara daga cikin gida ,mai inganci don ganin an rage shigo da ita daga kasashen ketare da dangogin ta , tare da bunkasa lafiyar al’umma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!