Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kungiyar manoma ta AFAN ta koka kan bada bashi na Noma

Published

on

Gamayyar kungiyoyin manoma  ta AFAN sun bukaci gwamnati tarayya da ta binciki ayyukan shirin baiwa manoma basuka da inshorar noma na NIRSAL.

Kungiyoyin sun bukaci hakan ne  a yayin wata ganawa da manema labarai da  suka gudanar a Abuja.

A wani yunkuri da sukayi don jawo hankalin gwamnati  kungiyoyin sun rike alluna masu rubutu, dake kiran  gwamnati ta binciki shirin kasancewar yana cike da almundahana da cutar da manoma a cewar kungiyar.

Labarai masu alaka.

Taimakon kai-da-kai shi ne mafi a’ala ga manoma – Kungiyan manoma ta Kano

An bude sabbin filayen noman rani a jami’ar Bayero

Daya daga cikin mamba na kungiyar  a nan jihar Kano Malam Buhari Kura, ya ce shirin karkashin bankin kasa CBN,ya maida hankali ne wajen baiwa manoma basuka, a wani mataki na bunkasa harkokin noman su, sai dai hakan ya bar baya da kura kasancewar shirin bai riksi manoman na aini hi.

Malam Shehu Umar, daya daga cikin kungiyar masu neman tumatur ya koka akan cewar babu dan kungiyar ko mutum daya da ya samu tallafin noma daga shirin na NIRSAL a shekarun da suka gabata.

An fito da tsarin ne da hadin gwiwar ma’aikatar noma da ci gaban karkara ta gwamnatin tarayya, da nufin samawa manoma sauki da bunkasa sana’oin noma a fadin kasar nan, tare da samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!