Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

NNPC ya gargadi jama’a su guji amfani da wani gurbataccen man Diesel

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ja hanakalin al’ummar kasar nan da su guji wani nau’in gurbataccen bakin mai wato man Diesel da ake sayarwa jama’a.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin na NNPC ya fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Kennie Obateru.

Sanarwar ta ce kamfanin na NNPC ya dau wannan mataki ne bayan samun korafe-korafe daga wajen jama’a game da nau’in man na DIESEL wanda ake sayar da shi da saukin kudi ga jama’a, a wasu sassan kasar nan.

NNPC:ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna da jami’ar Bayero

NNPC ta tallafawa Kano da kayan yakar Coronavirus

Kamfanin na NNPC ta cikin sanarwar dai ya kuma bukaci masu ababen hawa da sauran masu na’urorin da ke amfani da man Diesel da su rika yin takasansan wajen sayan man da za su yi amfani da shi.

Sanarwar ya kuma ruwaito kamfanin na NNPC na cewa, zai iya kokarinsa wajen ganin ya bankado batagarin da ke samar da man na Diesel gurbatacce domin daukar matakin da ya dace akansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!