Labarai
Bankunan kasuwancin kasar nan sun ƙara kuɗin tura saƙon kar ta kwana zuwa Naira 6

Bankunan kasuwancin kasar nan sun ƙara kuɗin tura saƙon kar ta kwana na SMS zuwa Naira 6, daga Naira 4 da ake biya a baya.
Karin kuɗin na kunshe ne a cikin saƙonnin da wasu bankuna suka aikewa abokanan huldar su a safiyar ranar Laraba, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Bankunan sun bayyana cewa ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin sadarwa da kamfanonin sadarwa suka sanar a baya-bayan nan.
Sai dai har yanzu babban Bankin kasa CBN bai fitar da wata sanarwa kan matakin ba, yayin da abokanan huldar ke bayyana damuwa kan yawan ƙarin kuɗin da suke fuskanta daga bankuna.
You must be logged in to post a comment Login